Ana bukatar matakan gaggawa domin magance satar bayanai

Shugabannin kamfanoni sun nemi a dauki matakan gaggawa domin magance matsalar masu satar bayanai a shafukan internet bayan harin da aka kai wa shafin Talk Talk, wanda suka ya ce yana daya daga cikin manyan barazana da kamfanoni ke fuskanta.

Cibiyar manyan directoci watau IOD ta ce manyan laifuka ne kadai kafofin watsa labari suke yadawa sai dai kusan ko yau she ake kai wa shafukan internet na kamfanonin Burtaniya hari.

Gwamnatin Burtaniyar dai ta ce a shirye ta ke ta shawo kan matsalar.

Da dama daga cikin masu amfani da shafin Talk Talk sun yi korafin cewa an shiga cikin asusun ajiye kudi na banki ko kartin bashi.

Wata mata da ke amfani da shafin na Talk Talk ta shaidawa BBC cewa ta yi asarar fam 600 da ke ajiye a cikin asusu kudi na banki ko da yake ta ce bankin ya ce zai biya ta kudin.

Haka kuma wata matar ta ce ita da mijinta sun rasa fam dubu 9 daga cikin asusun kudinsu, bayan da wani ya kira ta wayar tarho inda ya fake da cewa shi ma'aikacin Talk Talk a ranar Lahadi da kuma Talata.

Kamfanin Talk Talk ya ce ya soma gudanar bincike kan korafen korafen da masu amfani da shafin suka gabatar masa.

Ita ma hukumar 'yan sanda ta Butaniya ta ce ta soma gudanar da bincike kan lamari da kuma kudin fansa da wasu da suka yi ikirarin cewa su ne suka kai harin suka nema.