Ana ci gaba da kada kuri'a a Tanzania

Masu kada kuri'a a Tanzania
Image caption Jam'iyyar CCM ta mulki kasar fiye da shekaru 50.

Al'umar kasar Tanzania na kada kuri'a a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisu, wanda ake sa ran zai zama babban zabe tun bayan da gwamnati mai mulki ta jam'iyyar CCM ta kama aiki shekaru 50 da suka wuce.

Rahotanni sun bayyana cewa ana gudanar da zaben cikin lumana, yayin da a bangare guda kuma 'yan kasar suka fito kwansu da kwarkwatarsu a sa'o'in farko na fara kada kuri'a.

Shugaba Jakaya Kikwete ya sauka daga mukaminsa saboda cika wa'adin shugabanci sau biyu da kundin tsarin mulkin kasar ya ba shi damar yi.

Ana kuma sa ran dantakarar shugaban kasa na jami'iyyar CCM, John Magufuli shi ne zai lashe kuri'un, inda ya ke fafatawa da tsohon Firai Ministan kasar Edward Lowassa wanda a baya-bayan nan ya fita daga jam'iyyar CCM.

Dukkan 'yan takarar dai sun yi alkawarin magance matsalar coin hanci da rashawa da kuma kara samar da ababen more rayuwa a kasar ta Tanzania.