Shin ƙarfe nawa ne a Turkiyya ?

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wannan rudu ya sa ana yi wa shugaba Erdogan barkwanci

Jama'a a Turkiyya yanzu haka suna cikin rudani domin basu san ko menene takamaiman lokaci ba a kasar.

Hakan ta faru ne sakamakon jinkirta canza lokaci da aka saba yi.

A Turkiyya a daidai wannan lokaci ne ake maida agogo baya da sa'a guda kowacce shekara, amma bana gwamnatin shugaba Erdogan ta jinkirta canza lokacin har sai bayan zaben da za a yi ranar Lahadi domin baiwa masu kada kuri'a karin lokaci.

Na'aurorin dake nuna lokaci basu yi la'akari da umarnin kada a canza lokacin ba, wanda hakan ya haifar da rudani, har wasu a shafukan sada zumunta suna cewa, yanzu ana cikin lokaci ne na 'Erdogan'.