Amurka da Saudiyya na tattaunawa kan Syria

John Kerry a lokacin da ya isa kasar Saudi Arabiyya. Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kasashen biyu sun amince su hada karfi da karfe dan yakar kungiyoyin 'yan tawaye a Syria.

kasashen Amurka da saudiyya sun amince su kara zage dantse a abinda suka kira yakar kungiyoyin 'yan tawaye da ke yaki da shugaban kasar Syria Bashar al-Assad.

Bayan tattaunawa tsakanin sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, da sarki Salman na Saudi Arabia a babban birnin kasar Riyadh, jami'ai sun ce kasashen sun kuma amince da sake matsa lamba dan kawo karshen rikicin na Syria.

Tun da fari Rasha ta ce a shirye ta ke ta taimakawa 'yan aware da gwamnatin Amurka ke marawa baya na Free Syrian Army idan har za su yaki masu tada kayar baya na kungiyar IS da ke ikirarin kafa daular musulunci.

A makwannin da suka gabata dai 'yan aware na FSA na daga cikin wadanda Rasha ke kaiwa hari ta sama a kasar ta Syria.