Karancin mai ya soma dawowa a Nigeria

Image caption Motoci kan shafe sa'o'i a gidajen mai kafin su samu man

Rahotanni daga wasu sassan Nigeria na cewa matsalar karancin man fetur ta sake kunno kai, inda masu ababan hawa da sauran masu amfani da man ke shan wahalar samunsa.

Jihar Bauchi dai na daya daga cikin wuraren da ke fama da matsalar inda galibin gidajen mai ba sa sayar da man.

Wasu sun danganta matsalar a kan dilalan man fetur wadanda ba sa son su sayar da man abin da kuma dillalan man fetur din suka musanta.

Wakilin BBC a Bauchi ya ce a wasu wuraren ana sayar da man ne a kan naira 100 a kan kowacce lita a maimakon naira 87 da gwamnati da kayyade.

A Gusau babban birnin jihar Zamfara ma, wakilinmu ya ce ana sayar da man fetur din a wasu gidajen mai a kan naira 100 kowacce lita.

A baya-baya nan ne kamfanin mai na Nigeria watau NNPC ya gargadi 'yan bumburutu su daina siyan mai su na boyewa.

Image caption 'Yan bumburutu na cin kasuwa a Bauchi