Wane irin nama ne ke janyo ciwon daji ?

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani mahauci a Nigeria

Wani sabon rahoto da hukumar lafiya ta duniya WHO ta fitar, ya ce cin jan nama da naman gwangwani zai iya kara yiyuwar mutum ya kamu da cutar daji ko Kansa.

Sashen bincike a kan cutar Kansa na hukumar WHO din ya gudanar da bincike a kan naman gwangwani, ya kuma gano cewa cin gram hamsin na naman alade a kullum na haddasa karuwar samun cutar daji ta mafutsara da kashi 18 cikin dari.

Amma abun bai kai haka ba a kan jan nama, inda binciken ya dan nuna cewa cin jan nama zai haddasa cutar kansa.

Sai dai rahoton ya tabbatar da cewa cin nama na kara lafiya sosai ga jikin bil adama.

Naman da aka sarrafa shi ne wanda aka sauya dandanonsa ko aka saka wasu sinadirai domin ka da ya lalace.