Shin jiragen ruwan Rasha za su iya katse intanet?

Image caption Jirgin yakin Rasha na ruwa

Wani rahoto da jaridar New York Times ta buga ya ce akwai yiwuwar Rasha ta na yunkurin bullo da wasu dabaru na katse hanyoyin sadarwa na intanet a lokacin yake-yake nan gaba.

Rahoton ya ce wasu majiyoyi da dama na soji suna nuna damuwa game karuwar aikace aikacen sojojin ruwa na Rasha a kusa da inda aka ratsa da wasu muhimman wayoyi a karkashin ruwa.

Wayoyin suna da muhimmanci sosai ta wajen sadarwa ta intanet na yau da kullun, kuma suna dauke da muhimman bayanai daga wata nahiya zuwa wata.

Amma tambayar ita ce, shin jiragen yakin Rasha na ruwa suna yunkurin katse wadannan wayoyin ne?

Mista Keir Giles, wani jami'i ne na wani shiri da ya shafi Rasha a cibiyar Chatham House, kuma ya ce masu sa ido a kan take-taken Rasha sun dade da farga da wannan barazana.

Sai dai ya ce katse wa Amurka hanyoyin intanet abu ne da zai zamo da wahala, saboda yadda kasar ke da hanyoyin sadarwa na ciki da waje.

Amma Mista Giles ya ce akwai kasashen da za a iya katse wa hanyoyin sadarwa na intanet din.