Dangantakar Saudiyya da Biritaniya na cikin 'hadari'

Image caption Yarima Mohammed ya ce Saudiyya ta bayar da gagarumargudunmuwa tattalin arziki da harkokin tsaron Biritaniya.

Wani jakadan Saudiyya ya yi gargadin cewa duk wani "sauyin halayyar" Biritaniya game da Saudiyya, zai iya zuwa da "hadari mai tsanani".

Yarima Mohammed bin Nawaf bin Abdulaziz ya jaddada wannan gargadi a jaridar Daily Telegraph, inda ya bayyana cewa Biritaniya ta soke wata yarjejeniyar horas da ma'aikatan fursuna, da ta shiga da Saudiyya.

Ya kara da cewa shugaban jam'iyyar Labour, Jeremy Corbyn, ya "sabawa yarjejeniyar mutunta juna" inda ya bugi kirjin cewa shi ya haddasa soke yarjejeniyar.

Yarima Mohammed ya ce Saudiyya ta fi karfin a "koya mata darasi".

An dade ana zargin kasar Saudiyya da cin zarafin bil adama, inda Biritaniya ta ke matsin lamba a kan wasu hukunce-hukunce da suka shafi 'yan kasar da kuma baki.

'Rashin fahimta'

A farkon wannan watan ne, gwamnatin Biritaniya ta sanar da cewa ta fita daga yarjejeniyar fam miliyan 5.9 da Saudiyya, ta horas da ma'aikatan fursunonin kasar.

A wannan lokacin kakakin Firayi Ministan Biritaniya ya bayyana cewa gwamnati na bukatar ta mayar da hankali ga al'amuran cikin gida ne, dalilin da ya sa ta yanke shawarar fita daga yarjejeniyar kenan.

Yarima Mohammed ya yi korafin cewa kasar Saudiyya ta dade tana fama da rashin fahimta wurin kasashen duniya, amma yadda al'ummar Saudiyya suke mutunta dokoki da al'adu da kuma tsarin addinin Biritaniya, su ma suna bukatar Biritaniya ta daukaki na su.

Image caption Yarima Mohammed ya yi kwatanci da kalaman suka da shugaban jam'iyyar Labour Jeremy Corbyn ya yi.

A kwanan baya, dangantaka ta yi tsami tsakanin kasashen biyu sakamakon wani bako dan Biritaniya mai shekaru 74 da Saudiyya ta tsare bayan ta kama shi da barasa, inda har aka kusa zartar masa da hukuncin bulala 360.

Image caption An tsare Karl Andree, dan asalin Biritaniya a kasar Saudiyya, bayan an kama shi da barasar.

Mista Corbyn kuma ya nemi Firayi Minista Cameron, da ya sanya baki, domin Saudiyya ta sassauta hukuncin kisan da wani dan asalin Saudiyyar Ali Mohammed Baqir al-Nimr ke fuskanta, bayan an kama shi da laifuffuka da dama, ciki har da rashin yi wa sarki biyayya.

Yarima Mohammed dai ya bayyana cewa ba a yi wa kasar sa adalci ba wurin sukar da ta sha dangane da 'yan gudun hijirar Syria.

Inda ya ce Saudiyya ta karbi 'yan gudun hijirar Syria kusan miliyan biyu da rabi.