Shugaba Buhari zai halarci taro a Indiya

Hakkin mallakar hoto Reuters

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya zai halarci wani babban taron kasashen Afirka da ke gudana a birnin Delhi na kasar India.

Ministocin harkokin waje daga kasashen Afirkar da takwarar aikinsu ta India za su tattauna ranar Talata, a ci gaba da babban taron kasashen Afirka da India wanda ke gudana a birnin na Delhi.

Wannan ne dai na uku a jerin manyan tarukan da kasar ta India ta yi da kasashen Afirka, shi ne kuma mafi girma, wanda ake sa ran shugabannin kasar Afirka 35 za su halarta.

Mutane da dama dai na kallon wannan taro a matsayin wani yunkuri da India ke yi na gogayya da China a nahiyar Afirka.

Mataimaki na musamman ga shugaban Najeriya a kan al'amuran yada labarai, Malam Garba Shehu ya shaidawa BBC cewa batun zuba jari da bangaren kiwon lafiya na daga cikin abubuwan da Nigeria za ta fa'idantu da su daga wannan ziyara.