Biritaniya na horar da sojojin Nigeria

Hakkin mallakar hoto NIGERIA GOVT
Image caption Sojojin Nigeria na yaki da mayakan Boko Haram

Biritaniya na horar da sojojin Najeriya 150 dabarun yaki da ta'addanci.

Ana gudanar da wannan horo a makarantar horar da hafsoshin soji ta Najeriya da ke Jaji a jahar Kaduna.

Sojojin Biritaniya za su rika koya wa sojojin Nigeria masu mukaman Warrant Officers da na kasa da su dabarun kai farmaki da kai dauki, da sauran dabaru na yaki da tayar-da-kayar-baya.

Wannan dai wani shiri ne na hadin gwiwa tsakanin Biritaniya da Nigeria.

Manjo Janar Sanusi Mu'azu ya bayyana wa BBC cewa babu shakka horon zai inganta ayyukansu.

A yanzu haka dai Nigeria na yaki da kungiyar Boko Haram, yakin da ta lashi takobin kammala shi zuwa watan Disamba.