'Yan gudun hijira na bukatar agaji a Kamaru

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Boko Haram ta raba miliyoyin mutane da muhallansu

Hukumar 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya ta yi kira ga kasashen duniya su kai dauki zuwa kasar Kamaru domin tallafawa 'yan gudun hijira a cikin kasar.

Rahotanni sun ce a yanzu haka akwai 'yan gudun hijira fiye da 300,000 a cikin Kamaru wadanda suka guje wa tashin hankali a Nigeria da kuma jamhuriyar Afrika ta tsakiya.

A cewar jami'in na MDD Stephen O'Brien, a yanzu dubban mutane na cikin mawuyacin hali saboda rashin zaman lafiya a kasashensu na asali.

"Al'ummomi sun fice daga gidajensu, sun daina noma da ayyukan neman kudi saboda rashin tsaro da kuma hare-haren 'yan kunar bakin wake," in ji O'Brien.

Alkaluma sun nuna cewar a yanzu haka mutane kusan miliyan biyu ne a Kamaru da kewaye suke bukatar agajin gaggawa domin rayuwarsa ta inganta.