Zafi zai iya hana mutane zama a waje

Hakkin mallakar hoto SPL
Image caption Hayaki mai dumama yanayi

Wani bincike da aka gudanar a Amurka ya ce dumamar yanayi da ake samu za ta iya sa zafi ya karu a wasu sassan duniya ta yadda mutane ba zasu iya zama a waje ba.

Yanayi mai matukar zafi da kuma lullumi za su sa jikin mutane su kasa sanyayawa saboda zufa.

Binciken wanda kwararru daga cibiyar ilimin fasaha ta Massachusette suka gudanar ya bayyana kasashen larabawa a yankin gulf a matsayin inda zafin zai iya yin yawa.

Binciken ya nuna cewa zafi a wuraren zai yi matsanancin karuwa a karshen karni muddin ba a magance matsalar sauyin yanayi ba.

Wadanda suka wallafa binciken suka ce yakamata a rage hayakin da ake yawan fitar wa zuwa sararin samaniya domin ganin dumamar yanayi a duniya bai zamo mai cutarwa ba.