Ana taron tallafa wa 'yan hijira a Nigeria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu 'yan gudun hijira a Najeriya

A ranar Laraba ne ake shiga rana ta biyu ta taron da ake yi a Maiduguri kan yadda za a tallafa wa 'yan gudun hijira a arewa maso gabashin Najeriya.

Taron ya hada da masu ruwa da tsaki da suka hada da hukumomin tarraya da na jahohi da kuma kungiyoyi masu zaman kansu.

Shugaban kwamitin da zai nemi tallafin, Alhaji Muhammad Sani Zorro, ya ce za a dauki matakai na ganin cewa agajin da za a bayar ya kai ga wadanda aka bayar domin su.

Jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriyar na daga cikin jihohin da rikicin Boko Haram ya shafa.

Sai dai a daidai lokacin da ake wannan taro na tara tallafi ga 'yan gudun hijirar, wasu 'yan gudun hijirar daga jihar sun koka da cewa su ba su da sansanoni a cikin jahar.