Ouattara ya sake lashe zaben Ivory Coast

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaba Alassane Ouattara

Shugaban kasar Ivory Coast, Alassane Ouattara, ya sake lashe zaben shugaban kasar a karo na biyu.

Hukumar zaben kasar ta ce shugaba Ouattara ya yi nasara a zaben da a ka gudanar ranar Lahadi da fiye da kashi 83 cikin dari na kuri'un da aka kada.

Babban abokin hamayyarsa shi ne tsohon firayi ministan kasar, Pascal Affi N'Guessan, wanda ya samu kashi tara cikin dari na kuri'un, kuma ya yi takara ne a karkashin jam'iyyar IPF ta tsohon shugaba Laurent Gbagbo wanda Ouattara ya kayar da zaben shugaban kasar na shekarar 2010.

'Yan takara na jam'iyyun hamayya da dama sun fice daga yakin neman zaben inda suka yi korafin cewa ba za a gudanar da zabe na gaskiya ba.

Sai dai masu sa ido kan zaben sun ce sun gamsu da yadda zaben ya gudana.

Wannan dai shi ne babban zabe na farko tun bayan zabe mai zafi sosai da aka gudanar a kasar a 2010, wanda ya janyo barkewar yakin basasar da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 3000.