Shugabannin Afrika da suka fi dadewa a mulki

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaba Denis Sassou Nguesso na kasar Congo-Brazaville.

Jami'ai sun fitar da sakamakon zaben raba gardama a kasar Congo-Brazzaville, wanda ya nuna cewa sama da kaso 92 cikin dari na masu zabe sun amince da sauya kudun tsarin mulkin kasar da zai bai wa shugaban kasar damar sake takarar mulki a karo na uku.

A yanzu dai kudun tsarin mulkin kasar bai yadda Shugaba Denis Sassou Nguesso ya sake shiga takara ba, saboda shekarun sa sun wuce 70, kuma ya riga ya yi mulki sau biyu.

Sassou Nguesso ya hau mulki a shekarar 1979, inda face wasu shekaru biyar da ya yi ba a kan karargar ba, ya ke mulkin kasar.

Ga shugabannin da suka dade a kan mulki:

 • Shekaru 36 a kan mulki: Teodoro Obiang Nguema Mbasogo, shugaban kasar Equitorial Guinea. Ya zama shugaban kasar bayan juyin mulkin da aka yi a ranar uku ga watan Agustan shekarar 1979, inda kuma aka bayyana shi a matsayin shugaban kasa a ranar 12 ga watan Oktoba a shekarar 1982.

 • Shekaru 36 a kan mulki: Jose Eduardo dos Santos, shugaban kasar Angola. Shugaban jam'iyyar da ta kwatan ma kasar 'yancin ta daga hannun kasar Portugal a shakarar 1975, Dos Santos ya soma mulki tun a ranar 20 ga watan Satumbar shekarar 1982.

 • Image caption Shugaba Robert Mugabe na kasar Zimbabwe.

  Shekaru 35 a kan mulki: Robert Mugabe, shugaban kasar Zimbabwe. Shi ne kadai shugaban kasa a nahiyar Afrika da ya ke mulki tun lokacin da kasar sa ta samu 'yancin kanta, inda Mugabe ya zama Firayi Ministan a watan Afrilun shekarar 1980 daga bisani kuma ya zama shugaban kasar a shekarar 1967.

 • Hakkin mallakar hoto no
  Image caption Shugaba Paul Biya na kasar Kamaru.

  Shekaru 32 a kan mulki: Paul Biya, shugaban kasar Kamaru. Ya hau karagar mulki a ranar 6 ga watan Nuwambar shekarar 1982.

 • Shekaru 29 a kan mulki: Yoweri Museveni, shugaban kasar Uganda. Ya soma mulki a watan Junairun shekarar 1986, bayan sun yi nasarar a yakin da ya hambarar da gwamnatin Idi Amin Dada, da taimakon kasar Tanzania da ke makabtaka da su.

 • Shekaru 29 a kan mulki: Sarki Mswati III, shugaban kasar Swaziland. Ya hau mulkin masaurtar da ke kudancin nahiyar Afrika a watan Afrilun shekarar 1989, shekaru hudu bayan mahaifinsa ya rasu.

 • Hakkin mallakar hoto Reuters
  Image caption Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir.

  Shekaru 26 a kan mulki: Omar al-Bashir, shugaban kasar Sudan. Yana kan karaga tun bayan da ya kwace mulki a watan Yunin shekarar 1989.

 • Hakkin mallakar hoto
  Image caption Shugaba Idriss Deby na kasar Chadi.
  Shekaru 25 a kan mulki: Idriss Deby, shugaban kasar Chadi. Ya soma mulkin kasar a watan Disambar shekakar 1990, bayan hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar, Hissein Habre.

  Ga kuma shugabannin Afrika da suka fi dadewa a mulki a kasashen da aka yi wa mulkin mallaka a tarihin Afrika.

 • Sarki Haile Selassie, wanda aka tsige daga mulkin kasar Habasha a shekarar 1974, bayan ya shafe shekara 44 yana mulki.

 • Shugaban Libiya Moamer Gaddafi, wanda ya yi mulki kasar sa har kusan tsawon shekaru 42 bayan juyin mulkin da ya kawo shi a shekarar 1969. Tawayen da ya samu goyon bayan Turawa ya haddasa tsige Ghaddafi kuma aka kashe shi a shekarar 2011.