An kafa sabuwar runduna a Benisheikh

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rikicin Boko Haram ya daidaita jihar Borno

Rundunar sojin Nigeria ta yi karin haske a kan sabuwar runduna ta musamman ta ashirin da tara a garin Benisheikh da ke jihar Borno.

Kakakin rundunar sojin kasa ta Najeriya, Kanal Sani Usman Kukasheka ya ce "Akwai bataliyoyi a karkarkashin wannan runduna kuma za ta kasance da kayayyakin yaki domin kawar da Boko Haram."

"Muna samun nasarori a yakin kuma kara yawan makamai zai ba mu damar ci gaba da samun nasara," in ji Kukasheka.

Rundunar har wa yau ta jadda matsayinta na cewa babu wata karamar hukuma ta jihar Borno da ke hannun Boko Haram.

An ambato gwamnan jihar Borno Kashim Shattima na cewa akwai kananan hukumomin jihar guda biyu da har yanzu suke karkashin ikon 'yan kungiyar Boko Haram.

Su ma wasu 'yan jihar Bornon da ke gudun hijira, sun jaddada cewa bayanan da suke samu sun nuna cewa har yanzu yankuna da dama da 'yan Boko Haram ke iko da su a jihar.

Rikicin Boko Haram ya janyo mutuwar mutane fiye da 20,000 tare da raba wasu miliyoyi daga muhallansu.