Majalisa ta tantance karin ministoci biyar

Hakkin mallakar hoto Nigeria Senate
Image caption Amaechi na daga cikin wadanda aka tantance a makon da ya wuce

Majalisar dattawan Najeriya ta tantance karin mutane biyar da shugaban kasar ya mika mata domin nada su a matsayin ministoci.

Wadanda majalisar ta tantance su ne Farfesa Adewale Isaac Folorunso da Honourable Bawa Bwari Abubakar da Geoffrey Onyeama, da Zainab Shamsuna Ahmed da Birgadiya Janar Mansur Mohammed Dan’Ali da kuma Pastor Usani Uguru Usani.

Shugaba Buhari dai ya aike wa Majalisar da da sunayen mutane 37 domin a nada su ministoci, sai dai ya janye sunan Alhaji Ahmed Musa Ibeto daga jihar Naija, bayan da aka gano cewa sunayen mutane biyu aka mika daga jihar.

A makon da ya gabata ne majalisar dattawan karkashin jagorancin Sanata Abubakar Bukola Saraki ta tantance tsohon gwamnan jihar Ribas, Rotimi Amaechi da wasu mutanen.

Tuni majalisar ta amince da nadin mutane 18 daga cikin mutanen 37 domin bai wa shugaba Buhari damar rantsar da su a matsayin ministoci.

A ranar Laraba ake sa ran majalisar za ta ci gaba da aikin tantance ministocin.