Sojin Nigeria sun ceto mutane 338

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojojin sun ce suna ci gaba da kokarin murkushe kungiyar Boko Haram.

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun ceto mutane 338 daga hannun kungiyar Boko Haram a kauyuka daban-daban na jihar Borno.

A wata sanarwa da kakakin rundunar sojin kasa, Kanar Sani Usman Kukasheka ya fitar, ya ce mutanen da aka ceto sun hada da maza takwas da mata 138 da yara 192.

Ya kara da cewa an kai su garin Mubi da ke jihar Adamawa domin duba lafiyarsu.

Kanar Kukasheka ya ce dakarunsu sun kashe 'yan kungiyar boko Haram 30, sannan suka lalata manyan sansanoninsu a kauyuka hudu da ke kusa da dajin Sambisa.

Sanarwar ta kara da cewa sojojin sun kwato makamai daban-daban daga hannun 'yan kungiyar ta Boko Haram.