An soke zaben 'yan majalisar dokokin Ribas

Hakkin mallakar hoto no credit
Image caption A makon jiya ne aka soke zaben gwamna Wike.

Kotun da ke sauraren kararrakin zabe a Najeriya ta soke zabukan 'yan majalisar dokokin jihar Ribas guda 21 cikin su har da kakakin majalisar.

Dukkan 'yan majalisar dokokin 'yan jam'iyyar PDP ne.

Kotun, wacce ke zaman ta a Abuja, ta ce zaben 'yan majalisar na cike da kura-kurai

Da ma dai 'yan majalisa 32 ne a majalisar dokokin jihar ta Ribas.

A makon jiya ne wata kotun ta soke zaben gwamnan jihar, Nyesom Wike, tana mai cewa an tafka magudi a zaben sa .