An zargi Sudan ta Kudu da aikata laifukan yaki

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An zargi gwamnati da 'yan tawaye da aikata laifukan yaki.

Kungiyar Tarayyar Afirka ta zargi gwamnatin Sudan ta Kudu da 'yan tawayen kasar da laifukan yaki da na keta hakkin bil adama.

A wani bincike da kungiyar ta yi, wanda tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya jagoranta, ta bayyana yadda aka gallaza wa fararen hula, ciki har da yi musu fyade da tilasta musu cin naman mutane.

Sai dai rahoton ya ce babu wata alama da ke nuna cewa an ci zarafin mutanen ne saboda kabilarsu.

Rahoton ya kara da cewa rikicin kasar ya fara ne tsakanin sojojin da ke tsaron shugaban kasar, har ya kai gwamnati ta fara kashe 'yan kabilar Nuer.

Sai dai rahoton ya musanta cewa tsohon mataimakin shugaban kasar, Riek Machar, dan kabilar Nuer, ya yi kokarin juyin mulki.