An bayar da belin yaron da ya yi wa Talk-Talk kutse

Image caption Kamfanin sadarwa na Talk-Talk

An bayar da belin yaron nan dan shekara 15 da a ka kama a Ireland ta Arewa saboda ya yi wa kamfanin sadarwa na Talk Talk kutse.

'Yan sandan da ke binciken kutsen sun bincike gidan wani babban jami'in gundunar Antrim.

An kama yaron ne bisa zarginsa da laifin amfani da na'urar kwamfuta ta hanyar da bata dace ba.

Daga nan a ka wuce da shi ofishin 'yan sanda na gundumar Antrim inda jami'ai suka yi ta masa tambayoyi.

'Yan sanda suka ce an bayar da belin yaron zuwa watan Nuwamba, sai dai ba a tsayar da rana ba.

A cikin makon da ya gabata ne labarin kutsen da aka yi wa shafin intanet na kamfanin Talk Talk ya bazu.

Kamfanin wanda yake da mutane fiye da miliyan 4 masu mu'amala da shi a Burtaniya ya ce a lokacin kutsen, akwai yiwuwar an shiga rumbun adana bayanan masu mu'amala da kamfanin.

Sai dai kamfanin ya ce ba saci bayanan katin yin siyayya da cire kudi a banki na mutanen ba.