Ministoci tara sun sha kaye a Tanzania

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana ci gaba da tattara sakamakon zabe

Ministoci tara a gwamnatin kasar Tanzania sun sha kaye a zaben 'yan majalisar dokokin kasar, a yayin da aka soma fitar da sakamakon zaben da aka kada a ranar Lahadi.

Wannan sakamakon bai yi wa jam'iyya mai mulkin kasar dadi ba, saboda hadakar jam'iyyar 'yan adawa ta Ukawa ce ta samu wadannan kujerun.

Wakilin BBC a Dar es Salaam, ya ce a yanzu haka dai jam'iyyar CCM wacce ta shafe shekaru 54 a kan mulki ta shiga damuwa saboda wadannan sakamakon na farko da aka soma fitarwa.

Daga nan zuwa ranar Alhamis ake sa ran za a samu cikakkun alkaluma na sakamakon zaben.

Masu sa'ido na kungiyar tarrayyar Turai sun ce an gudanar da zaben lami lafiya.