Me ya sa Sarki ya cire Ciroman Kano ?

Image caption Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na 2

Majalisar masarautar Kano da ke Najeriya ta sauke Alhaji Lamido Ado Bayero daga sarautar Ciroma.

Wata sanarwa da majalisar ta fitar ta bayyana cewa an cire tsohon Ciroman ne saboda ya ki yi wa Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II mubaya'a tun da ya zama Sarki a watan Yunin bara.

Sanarwar, wacce ke dauke da sa hannun Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi, ta ce an maye gurbin Ciroma ne da kanensa, Turakin Kano Alhaji Nasiru Ado Bayero wanda yanzu shi ne sabon Chiroman Kano.

Tsohon Ciroman Kanon, Alhaji Lamido Ado Bayero, shi ne mutumin da ya yi takarar neman sarautar Kano da Sarki Sanusi Lamido, bayan mahaifinsa Alhaji Ado Bayero ya rasu.

Tunda ya rasa kujerar Sarkin Kanon, majalisar masarautar ta ce bai yi mubaya'a ga sabon Sarkin ba.