Iran za ta halarci taro kan Syria a Vienna

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wasu 'yan Iran na goyon bayan Syria

Ma'aikatar harkokin wajen Iran ta ce kasar za ta halarci taron da za'a yi a kan Syria a wannan makon.

Ta ce ministan harkokin waje, Mohammad Javad Zarif zai je wajen tattaunawar da za'a yi a Vienna a ranar Juma'a.

Wannan shi ne karon farko da Iran - wadda babbar mai goyan bayan shugaba Assad ce - za ta halarci wani taron zaman lafiya na kasa da kasa a kan Syria.

Iran dai wata babbar mai goyan bayan shugaba Assad ce kuma kamar Rasha, ita ma Iran din kwananan ta kara zafafa rawar da take takawa ta fuskar soji wajrn yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda.

'Yan adawar Syria sun ce zuwan Iran wajen tattaunawar a Vienna zai kara dagula al'amura ne kawai.