'Yan majalisar wakalai sun raba gari

Hakkin mallakar hoto DOGARA TWITTER
Image caption Shugaban majalisa, Yakubu Dogara

A Najeriya, rabon mukaman shugabancin kwamitocin majalisar wakilan kasar da kakakinta, Yakubu Dogara, ya yi ya raba kawunan 'yan jam'iyya mai mulki ta APC da ke majalisar.

A ranar Alhamis ne dai Yakubu Dogara ya sanar da sunayen shugabannin kwamitocin majalisar 96, inda ya bai wa jam'iyyar APC 48, sannan ya bai wa PDP 46, sai kuma jam'iyyun SDP da APGA kowacce dai- dai.

Sai dai yawancin 'yan jami'iyyar APC na sukar yadda kakakin majalisar ya raba mukaman.

Wasu daga cikin 'yan jam'iyyar APC sun yi zargin cewa ko bayan yi wa jami'iyyar rashin adalci wajen rabon, ya kuma bai wa jam'iyyar hamayya ta PDP kwamitocin da suka fi "maiko."

Sai dai Shugaban kwamitin watsa labarai na majalisar ya shaida wa BBC cewa babu wani fifiko da aka bai wa 'yan jam'iyyar adawar ta PDP.