YouTube zai biya wadanda aka kalli bidiyonsu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shafin YouTube

Shafin YouTube zai biya wasu mamallakan hotunan bidiyo da mutane suka biya kudi kafin su kalla, a lokacin da shafin ya yi gwajin tsarinsa na karbar kudin kallo a wurin jama'a.

A ranar Laraba ne shafin na YouTube ya kaddamar da tsarin biyan kudi a wata a Amurka kafin mutane su kalli wasu hotunan bidiyo da shafin ya cire tallace-tallace a cikinsu.

Shahararrun masu sanya hotunan bidiyo a shafin na YouTube sun nuna damuwa kan cewa shafin ba zai biya su ba idan ya karbi kudi daga wurin jama'a na kallon bidiyonsu a wata daya da zai yi yana gwaji.

Masu sanya hotunan bidiyo a shafin YouTube suna samun kudade daga tallace-tallacen da ake nunawa a cikin bidiyon, amma sabon tsarin da shafin ya bullo da shi, ya cire tallace-tallace a Amurka saboda biyan kudi da jama'a suka yi.

A maimakon samun kudade daga tallace-tallacen, shafin na YouTube zai dan nuna musu hotunan bidiyon da aka kalla kadan daga cikin kudin da ya samu, gwargwadon mintocin da aka kalle su.