An soke zaben shugaban Zanzibar a Tanzania

Image caption 'Yan adawa sun soki matakin hukumar zabe

Hukumar zabe a yankin Zanzibar na kasar Tanzania ta soke zaben shugaban kasar yankin da aka yi ranar Lahadi kuma ta ba da umarnin sake gudanar da sabon zaben.

Shugaban hukumar zaben, Jecha Salim Jecha ya ce an tabka magudi sai dai kuma jam'iyyar adawa ta Civic United Front ta ce an kwace mata damar samun nasarar a tsibirin Tanzania da ke da dan kwarya - kwaryar cin gashin kai.

Tuni jam'iyyar CCM mai mulkin kasar ta Tanzania ta shigar da kara a kan dan takarar jam'iyyar CUF din a Zanzibar, Seif Sharif Hamad, kan bayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaben.

Akwai rahotannin cewa 'yan sanda sun harba hayaki mai sa kwalla domin tarwatsa masu zanga zanga.

Da yawan ministocin gwamnatin Tanzania sun rasa kujerunsu a zaben na ranar Lahadi.