DroidJack: 'Yan sanda sun yi samame a kasashen Turai 5

Image caption 'Yan sandan kasashen Turai

'Yan sanda sun kai samame a wasu gidaje a kasashen Turai biyar a wani bangare na binciken amfani da wata kinibabbiyar manhaja mai cutarwa.

'Yan sandan a Burtaniya da Jamus da Faransa da Belgium da kuma Switzerkand sun bincike wasu kayayyaki masu alaka da masu amfani da manhajar mai cutarwa da ake kira DroidJack.

Manhajar DroidJack ta na bai wa bata garin mutane damar yin leken asiri a manyan wayoyin salula, da sauraron hirarrakin sirri na mutane, da kuma yin kutse cikin na'urar daukan hoton wayoyin mutane.

Manhajar kuma ta na kutsen ne kadai a wayoyin Android, kuma ta na iya sanin duk abin da masu wayoyin suke yi ba tare da sun sani ba.

Wadanda ake zargi da amfani da manhajar 'yan shekaru 19 ne zuwa 50, kuma kawo yanzu, babu wanda aka kama daga cikinsu.

Gidaje 13 ne a Jamus da kuma daya a Switzerland ne 'yan sandan suka je.