Rikicin Syria wani bala'i ne — Kerry

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya ce yunkurin lalubo hanyar kawo karshen rikicin Syria, ba komai ba ne illa neman mafita daga bala'i.

Mista Kerry ya sanar da hakan kafin ya halarci wata tattaunawa a Vienna, inda zai hadu da ministocin waje na wasu kasashe da suka hada da Rasha da Saudiya da kuma a karon farko, Iran.

Ana sa ran tattaunawar ta ba da karfi a kan irin rawar da shugaban Syrian Bashar Al-Assad zai taka wajen sauya gwamnatin kasar.

Saudiyya da wasu kasashen yammacin duniya na kallon Shugaba Assad a matsayin mai hana-ruwa-gudu a yunkurin kawo karshen rikicin kasarsa, yayin da Rasha da Iran suke gani yana da muhimmiyar gudunmuwa da zai bayar a warware rikicin.

Mista Kerry ya yi gargadin cewa tattaunawar a wannan karon, ba za ta kawo masalaha a siyasance cikin gaggawa ba, amma dai wata babbar dama ce ta warware matsalar a nan gaba.