Wa'adin rijistar BVN a Nigeria ya cika

Image caption Wasu 'yan Najeriya dake bin layi a banki

A Nigeria, ranar Juma'a ne wa'adin da babban bankin kasar ya bayar na kammala rijistar masu asusun ajiya a bankunan kasar domin samun lambar BVN ke cika.

Kimanin mutane miliyan 21 ne ya zuwa yanzu suka yi rijista a bankuna daban-daban na kasar.

Babban bankin Najeriyar dai ya ce an dauki matakin yin rijistar masu asusun ajiya a bankunan ne a wani mataki na inganta harkokin bankunan kasar.

Malam Ibrahim Mu'azu, daraktan yadda labarai a babban bakin kasar, ya ce rijistar za ta saukake wa mutane hada-hada da banki saboda za su samu damar yin harkokinsu a duk inda suke ba sai sun je banki ba.

Ya ce rashin rijistar zai sa dole sai mutane sun rika zuwa banki da kansu, domin ba lallai ba ne a bar su, su rika cire kudi daga naurar ATM.

Sai dai Mallam Mu'azu ya ce mutanen da basu samu yin rijistar ba zasu iya zuwa bankin da suke amfani da shi domin yin rijistar.