Muhawarar 'yan takarar Republican a Amurka

Image caption 'Yan takara masu neman tikitin jam'iyyar Republic a Amurka

Masu neman tikitin jam'iyyar Republican a takarar shugabancin Amurka sun ci gaba da bayyana manufofinsu da suka sha bamban, a zagaye na uku na muhawarar da suke yi wadda ake watsawa ta talabijin.

Biyu daga cikinsu da ke gaba-gaba, Donald Trump da Ben Carson ba su koda kansu sosai ba, kamar yadda sauran 'yan takarar takwas suka yi.

Har yanzu babban dan kasuwa Donald Trump ne ke kan gaba, yayin da Ben Carson, tsohon likitan fida ke kokarin cimma sa a 'yan makonnin nan.

Wasu karin biyu daga cikin masu neman tikitin jam'iyyar ta Republican, Sanata Marc Rubio da Sanata Ted Cruz sun caccaki kafafen yada labarai, da masu gudanar da mahawarar saboda tamboyin da suka yi musu.

Shi kuwa tsohon gwamnan Florida Jeb Bush, kokari ya yi a ji na sa manufofin, yayin da gwamnan Ohio John Kasich ya caccaki wadanda suke gaba-gaba a neman tikitin jam'iyyar da abin da ya kira manufofinsu na almara.

Mace daya tilo a jerinsu, Carly Fiorina, wacce tsohuwar shugabar kamfanin kwamfutar HP ce, ta soki abin da ta kira manufofin 'yan jari hujja a kasar, sannan ta sha alwashin rage yawan shafukan kundin tsarin biyan haraji na Amurka daga shafuka dubu 73 zuwa uku kacal.