Rundunar sojin Afrika na shirin soma aiki

Dakarun sojin Afrika wacce aka kirkiro da nufin taimakawa nahiyar da duk wata matsala da za ta taso, za ta fara aiki bayan shekaru 13 da kaddamar da ita.

Daga watan Junairun shekarar 2016 ne, 'African Standby Force' (ASF) za ta sanya baki a rikice-rikicen da ke da alaka da laifuffukan yaki da kisan kare dangi da cin zarafin bil adama, idan har kasashen da ke cikin kungiyar Tarayyar Afrika watau AU, ko ita kanta Kungiyar Tarrayar Afrika ta bukace su da yi.

Dakarun za su kuma taimaka wurin kai dauki ga al'umma da aikin kawo zaman lafiya da sa ido wurin gudanar da ayyukan ceto, duk da cewar kai daukin zai dangana da gudunmuwar da kasashe suka bayar.

Rundunar da ta samu horo daban-daban, ta tanadi sassa guda biyar, kowanne da 'yan sanda da soji da fararen hula, kuma duk za a iya tura su yankuna cikin kwanaki 14.

Image caption Yanzu ana iya tura dakaru 17 zuwa yankuna daban-daban.

Birnin Douala da ke kasar Kamaru, shi ne zai zama ma'adanar kayayyakin aikin, amma manyan hafsoshin za su kasance ne a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, inda hedikwatar Tarayyar Afrika ta ke.

A yanzu an tura dakarun soji 5,000 daga kasashen daban-daban na Afrika zuwa kasar Afrika Ta Kudu, domin gudanar da aikin horon da zai tabbatar da cewa dakarun a shirye suke.

'Yaki da ta'addanci'

Yanayin tarzomar ya tashi daga rikice-rikice tsakanin mayakan sa kai da ke kokarin karbar ikon yankunan da ke da albarkatun kasa ko kuma domin hambarar da gwamnatin da ke mulki, zuwa ga ta'addancin mayakan da ke ikirarin kishin musulunci.

Image caption Aikin da rundunar hadin gwiwa ta ASF ke gudanarwa game da yaki da ta'addanci, zai iya kawo karin tallafi daga wurin masu bayarwa.

Rundunar ta ASF, wacce a yanzu dakarunta sun karu daga 8,000 a shekarar 2007 zuwa sama da 22,000, ta yi kokarin 'yanta garuruwa da birane da dama daga hannun mayakan Al-shabab.

Duba ga yadda rikice-rikicen Boko Haram ke kara yaduwa a yankunan arewa maso gabashin Najeriya, inda sansanonin su yake, ya sa aka sake kirkiro da wata sabuwar rundunar hadin gwiwa da ke da goyon bayan kungiyar Tarayyar Afrika.

Kaddamar da wannan rundunar hadin gwiwa ta ASF, za ta kawar da bukatar kafa wata sabuwar runduna a duk lokacin da wani rikici ya taso.

Duk da haka dai ASF tana fuskantar wasu matsaloli, wanda mafi girma cikin su, shi ne tallafi na kudi, inda har yanzu Kungiyar Tarayyar Turai ke bukatar dala biliyan daya domin gudanar da aiki.

"An yi ingantaccen aiki wurin gudunmuwar kai daukin zaman lafiya a nahiyar, " In ji Peter Pham, daraktan Africa Center of the Atlantic Council.

Image caption ASF tana fuskantar matsalolin rashin samun kayan aikin na jiragen sama.

Ya kara da cewa, "Ba a gano hikimar horo mai inganci ba tukuna a Afrika, misali tafiyar da sojin kasa na kasashe daban-daban su gudanar da aiki daya na da matukar wahala, ba kamar inda za a sa su gudanar da ayyuka daban-daban da zai tallafa masu duk a tare ba".