CAR: 'Ana yi wa zabe zagon kasa'

Hakkin mallakar hoto Reuters

Shugabar rikon kwaya a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta bayyana cewa zabuka na da mahimmanci ga makomar kasar- amma ta yi gargadin cewa akwai wadanda ke kin zaman lafiya dake kokarin hana aukuwar zabubbukan.

An dai soke zabukan ne bayan wani tashin hankali da ya barke tsakanin Kiristoci da Musulmi a babban birnin kasar na Bangui a watan Satumba ya yi sanadiyyar asarar rayuka 40

A wata hira da BBC Shugabar rikon kwaryar Kasar Catherine Samba Panza ta bayyana cewa ko da ace wasu 'yan siyasar kasar sun ki shiga cikin shirin da ake na yin zaben, jamhuriyar Afirka ta Tsakiya na kan hanyar gudanar da zaben

Za a gudanar da zabukan ne a watan Disamba