An kafa kwamiti kan zargin fyade a Kano

Image caption Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Gnaduje

Gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta kafa wani kwamiti domin binciken zarge-zargen yi wa yara dalibai fyade a makarantar Hassan Gwarzo.

Farfesa Abubakar Mustapha, tsohon shugaban jami'ar Maiduguri shi ne zai jagoranci kwamitin mai wakilci daga ma'aikatan gwamnati da masarauta da jami'an tsaro da lauyoyi da kuma kungiyoyin kare hakkin bil'adama.

An ba wa kwamitin makonni biyu domin mika sakamakon binciken.

Abubuwan da kwamitin zai yi sun hada da binciken gaskiyar al'amari da wadanda aka yi wa fyaden da wadanda suka yi da kuma ko makarantar tana da hannu a ciki ko ba bu.

Wannan dai yana zuwa ne 'yan sa'o'i bayan da gwamnatin jihar ta Kano ta bayar da umurnin rufe makarantar.

A ranar Alhamis ne wasu daliban makarantar da iyayensu suka yi zargin cewa wasu daliban na yi wa yaran fyade ko kuma a wasu lokutan yunkurin yi musu fyaden.

Sai dai hukumomin makarantar sun musanta zargin yin fyade a makarantar.