'Zargin uwa ta sayar da jariri a Cross Rivers'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan sanda sun damke mutane shida kan lamarin

'Yan sanda a jihar Cross River da ke kudancin Nigeria sun kama wata mata 'yar shekaru 20 tare da wasu mutane biyar bisa zargin sayar da jariri dan makonni biyu da haihuwa.

Matar -- wacce 'yar asalin karamar hukumar Odukpani ne a jihar -- ta ce talauci ne ya tallasta mata sayar da jaririnta a kan naira dubu dari biyu.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Cross River, John Eluu, ya shaida wa BBC sun soma gudanar da bincike a kan lamarin kuma naira dubu ashirin kacal aka bai wa matar.

Matsalar sayar da jarirai babbar matsala ce a yankin kudancin Nigeria inda a lokuta da dama akan kama mata da 'yan mata bisa zargin hada baki wajen cinikin jarirai.

Hukumomi a yankin dai sun sha alwashin kawo karshen wannen mummunar dabi'ar amma kawo yanzu lamarin na neman ya gagari kundila.