Kotu ta ki amincewa da bukatar Saraki

Image caption Kotun da'ar ma'aikata za ta shigaba da gudanar da shari'ar Saraki.

Kotun daukaka kara dake zama a Abuja babban birnin Najeriya, ta yi watsi da daukaka karar da shugaban majalisar dattawan Abubakar Bukola Saraki ya yi a gabanta, yana neman ta dakatar da kotun da'ar ma'aikata ta kasar, daga ci gaba da yi masa shari'a.

Senata Bukola Saraki dai na fuskantar zargin yin karya wajen bayyana kadarorin da ya mallaka lokacin da ya zama gwamnan jihar Kwara a gaban kotun ta da'ar ma'aikata .

Amma a zaman da ta yi yau da safe, kotun ta ce karar da aka shigar kansa, an shigar da ita ne bisa ka'ida kuma kotun ta da'ar ma'aikatan na da hurumin yi masa shari'a.

Sai dai lauyoyin Bukola Sarakin sun ce za su daukaka kara zuwa kotun koli.