Sudan ta koka da barayin shanu daga Habasha

Hakkin mallakar hoto Reuters

Rahotanni daga Sudan sun ce an sami karuwar tashin hankali na rikicin iyaka tare da Habasha.

Ministan cikin gida na Sudan Ismat Abdul Rahman ya fadawa majalisar dokoki cewa masu satar shanu 'yan Habasha sun kashe akalla manoma 16 sannan sun sace shanu kusan 300 a wasu farmaki da suka kai na baya-bayan nan

Mambobin majalisar dokokin Sudan sun nemi gwamnati ta tura sojoji zuwa jihar al-Qadarif da ke kan iyaka

Habasha da Sudan tuni suka amince su kafa wata hukuma domin shata iyaka