Mun samu kwarin gwiwa kan Syria — MDD

Image caption Sakatare Janar na MDD Ban Ki-moon

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya ya ce ya samu kawarin gwiwa da yadda a karon farko, kasar Iran ta shiga a dama da ita a tattaunawar kasa da kasa don kawo karshen rikicin kasar Syria.

A daidai lokacin da manyan kasashen duniya ke shirin fara muhimmiyar tattaunawar a Vienna, Mista Ban Ki-moon ya buka ce su da su nuna jagoranci na gari.

Mista Ban Ki-moon ya yi fatan cewa kasashen dake goyon bayan bangarorin da basa gama ciji da juna a rikicin na Syria, za su aje son zuciyarsu a gefe, su tattauna abin da ya dace a wurin taron.

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya yi tattaunawar share fage da takwarorinsa na Iran da Rasha da Turkiya da kuma Saudiya.

Fiye da kasashe goma sha biyu ne zasu hadu a yau Juma'a, a tattaunawar da ake gani kodai ta bude kofar warware rikicin na Syria, ko kuma ta kara rinchaba rikicin.