Jirgin Rasha ya yi hadari a Sinai

Iyalan wasu fasinjojin jirgin Rasha da ya yi hadari a Sinai Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Iyalan wasu fasinjojin jirgin Rasha da ya yi hadari a Sinai

Masu aikin ceto sun gano tarkacen jirgin a wani yankin tsaunuka a tsibirin Sinai.

Jami'ai a Masar sun ce dukkan mutanen da ke cikin jirgin sun rasa rayukansu.

Rahotanni daga wurin da hadarin ya faru na cewa akwai gawarwakin mutane da dama a kasa yayinda wasu suke makale a jikin kujrarsu.

Jirgin kirar Airbus A-321 ta taso ne daga Sharm el-Sheikh zuwa St Petersburg.

Wasu rahotanni sun ce jirgin ya yi kokarin saukar gaggawa a filin jirgin sama na El Arish a arewacin Sinai sakamakon matsalolin naura.

Hukumomin Masar sun ce dukkan fasinjojin yan kasar Rasha ne.

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya baiyana ailhininsa ga iyalan wadanda suka rasu yana mai cewa Rasha za ta tura masu aikin ceto zuwa Masar.