Boko Haram sun kai hari wasu kauyuka a Chadi

Hakkin mallakar hoto AFP

Maharan sun kashe sojoji biyu tare da jiwa wasu mutanen goma sha daya kuma raunuka.

Hukumomin suka ce a daya daga cikin harin sojoji sun sami nasarar harbe wasu mahara uku wadanda suka yi yunkurin kai harin kunar bakin wake.

An harbe mutanen ne yayin da suka tunkari wani sansanin soji.

Sai dai wani maharin ya tada bam din da yake dauke da shi.

Hukumomin Chadin sun kara da cewa da sanyin safiyar yau wasu wadanda ake zargin yan Boko Haram ne sun kai hari wani barikin soji a yankin.chad