Karancin man fetur ya tsananta a Bauchi

Image caption Mai yana wahala a wasu sassan Najeriya

Rahotanni daga jihar Bauch da ke arewa maso gabashin Nijeriya na cewa jama'a musamman masu ababan hawa da matafiya na ci gaba shiga mawuyacin hali sanadiyar karuwar karancin man fetur da kuma tsadarsa.

An ce dai masu ababan hawa a Bauchin suna ta faman wtangaririya domin neman man idan kuma sun samu to tsadarsa kan hana wasu siya.

Ko a kasuwar fage ko kuma wadanda aka fi sani da 'yan bunburutu ana yin dogon layi ne domin samun man duk kuwa da tsadarsa.

Yanzu haka kakar masu bunburutun ta yanke saka ne domin suna sayar da galan daya na man akan naira dari takwas zuwa da hamsin.

Wasu daga cikin masu sana'ar ta bunburutu sun shaida wa BBC cewa suna hana idanunsu barci domin neman man.