'Yan hamayya sun yi zanga-zanga kan zabe a Nijar

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaban Niger, Muhamadou Issoufou yana fuskantar matsin lamba daga 'yan adawa

Gamayyar jam'iyyun hamayya ta FPR a Jamhuriyar Nijar ta gudanar da wani gangami na neman gwamnatin Shugaba Mahamadou Issoufou ta tabbatar ta shirya sahihin zabe a 2016.

Magoya bayan 'yan hamayyar dauke da kwalaye masu rubutun cewa "Al'umma ta tashi tsaye tsayin daka don ganin an yi zabe na gaskiya" sun bukaci a yi cikakken nazari a kan rajistar masu zabe.

'Yan hamayyar dai sun sha yin suka a kan shirye-shiryen zaben, suna zargin cewa gwamnati ba ta yi niyyar shirya zabe na gaskiya ba.

Sai dai gwamnatin ta musanta zargin, tana mai cewa wannan batu bai ma taso ba.

A farkon shekarar 2016 ne kasar ta Nijar za ta gudanar da babban zabe.

Shugaba Muhammadou Issoufou yana neman sake tsaya takara karo na biyu duk kuwa da cewa yana fuskantar suka daga jam'iyyun hamayya.