Mun kashe 'yan BH hudu — Sojin Najeriya

Makarantar firamare ta Duwabafi a Jihar Bornon Najeriya
Image caption Sojojin Najeriya sun ce mayakan na boye ne a makarantar firamare ta Duwabafi

Rundunar sojin kasa ta Najeriya ta ce mayakanta sun kashe wasu 'yan bindiga hudu da suke zargin 'yan kungiyar Boko Haram yayin wani ba-ta-kashi jiya Lahadi.

Wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin rundunar, Kanar Sani Usman Kuka-Sheka, ta ce sojojin na Najeriya sun yi kicibis da mayakan ne a wata makarantar firamare da ke kauyen Duwabafi na Jihar Borno yayin da suke sintiri a yankin.

Kanar Kuka-Sheka ya kara da cewa dakarun sun kuma kwace bindigogi biyu kirar AK-47, da farantan samar da wutar lantarki daga hasken rana, da kwayoyin magani iri daban-daban, da kuma babura guda biyar.

Sanarwa na dauke da wadansu hotuna na makarantar da na kayayyakin da aka kwace, da kuma na wani mutum yana kwance cikin jini.

Sai dai kuma babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan labarin.

Karin bayani