'Akwai man fetur dankam a arewacin Nigeria'

Hakkin mallakar hoto google
Image caption Gwamnan jihar Bauchi, Barista Muhammad Abubakar

Gwamnan jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya, Barista Muhammad Abdullahi Abubakar, ya ce akwai man fetur mai yawan gaske a shimfide a yankin arewacin kasar.

A wata hira da ya yi da BBC, Barista Muhammad ya ce idan dai har za a samu mai a makwabtan Najeriya kamar Jamhuriyar Nijar da Chadi, to bai ga dalilin da zai sa a ce babu man a arewacin kasar ba.

Ya kara da cewa yanzu haka yana tattaunawa da katafaren kamfanin nan na man fetur na kasar Rasha watau Gasprom domin duba yadda za a fara aikin man fetur a yankin.

Jihar Bauchi na daya daga cikin jihohin arewa maso gabashin Nijeriya da ake kyautata zaton suna da arzikin man fetur a karkashin kasa.

A halin yanzu dai tattalin arzikin Nijeriya ya dogara ne kusan kacokan a kan albarkatun man fetur.

Sai dai wannan yunkurin na gwamnonin arewacin Najeriya na zuwa ne a dai-dai lokacin da farashin man yake ci gaba da faduwa warwas a kasuwar duniya.