Wata tawaga ta masu bincike ta isa Masar

Jirgin saman Rasha da ya yi hadari a Masar
Image caption Jirgin saman Rasha da ya yi hadari a Masar

Wani ayarin masu bincike daga Rasha ya isa kasar Masar domin gano musabbabin hadarin da jirgin Rashar ya yi a yankin Sinai ranar Asabar, wanda kuma ya yi sanadiyyar dukkanin mutane 224 da suka kasance a cikin jirgin.

Jami'an kasashen na Rasha da Masar sun yi watsi da ikirarin da kungiyar IS tayi cewa ita ce ta harbo jirgin.

Fira ministan Masar Shariff Ismail ya ce watakila injin din jirgin ne ya samu matsala.

Jamian gwamnatin Masar sun ce an gano naurar nadar bayanai na jirgin saman kuma an soma nazari akansu.

Sai dai wasu jiragen sama uku da suka hada da Emirates da Airfrance da kuma Lufthansa sun yanke shawarar cewa jiragensu za su daina bin yankin Sinai har sai an samu karin haske akan abin da ya faru.

Jirgin sama mallakar na kamfanim Kogalymavia samfarin Airbus A 321 mai dauke da fasinjoji sama da 200 ci ki har da yara kanana 25.