Bam ya hallaka mutane 7 a Somalia

Hakkin mallakar hoto AFP

Da asuba bam din ya tashi kuma wasu mazauna birnin Mogadishgu sun ce sun da de basu ji kara mai karfin gaske irin wannan ba.

Sai dai an dinga jin karar harbe harben bindigogi ya yinda jamian tsaro suka yi bata kashi da wasu 'yan bindiga da ake zargin mayakan kungiyar Al shabab ne da ke kokarin shiga cikin ginin.

Haka kuma ana kyautata zaton cewa manyan masu karfin fada a ji na kasar da ke cikin otel din sune aka kai wa harin.

Harin dai na zuwa ne bayan arrangamar da mayakan Alshabab suka yi da dakarun hadin gwiwa a yankin Bakool na kasar ta Somalia.

A baya baya nan ne wani reshe na kungiyar Al shabbab ya yanke kawance da kungiyar Al qaeda inda ya yi wa kungiyar IS mubayi'a.