'Yan tawayen Sudan ta kudu sun rike maaikatan MDD

Hakkin mallakar hoto Reuters

Jami'an wadanda ke yi wa Majalisar Dinkin Duniyar aikin kwantaragi an yi garkuwa da su ne daga cikin wani jirgin ruwa kusa da birnin Malaka a makon da ya wuce.

'Yan tawayen sun ce suna tsammanin mutanen suna kaiwa sojojin gwamnati makamai ne.

Duk da cewa bangarorin da ke gaba da juna a Sudan ta Kudu sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya a watan Augusta, har yanzu ana cigaba da fafata fada a yankin Unity da Upper Nile mai arzikin mai da bangarorin ke takaddama akai.