'Boko Haram na ƙera makaman roka'

Hakkin mallakar hoto Boko Haram

BBC ta samu wasu hotuna da ke nuna wani wuri kamar masana'antar kera makamai ta kungiyar Boko Haram.

Hotunan sun nuna makaman roka sababbi da aka kera da injinan wata makaranta da ake zaton kwalejin gwamnati ce da ke garin Bama a jihar Borno.

An aiko da hotunan ne ta lambar WhatsApp na sashen Hausa na BBC.

Hakkin mallakar hoto Boko Haram

A jikin wasu daga cikin hotunan akwai tambarin kwalejin Bama watau GTCB, inda wasu daga cikin mayakan Boko Haram ke sarrafa wasu manyan injuna na hada makaman roka.

Kungiyar Boko Haram ta taba kwace iko da garin Bama kafin dakarun gwamnatin Nigeria ta sake kwace garin.

Bisa dukkan alamu asusun tallafa ilimi na gwamnatin tarraya ne (ETF) ya samar da manyan injunan ga kwalejin a shekara ta 2005.

'Sarrafa Injuna'

Hakkin mallakar hoto Boko Haram

Sai dai babu tabbas a kan lokacin da aka dauki hotunan.

An dade ana mahawara a kan inda 'yan Boko Haram ke samun makamai saboda kungiyar tana amfani da makaman roka a lokacin fafatawa da sojojin Nigeria.

Abin da ke kara jefa fargaba a zukatan jama'a shi ne yadda wasu daga cikin mayakan ke iya sarrafa injuna domin kera makamai.

Shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari ya bai wa sojojin kasar wa'adi zuwa karshen watan Disambar bana domin su kawar da kungiyar Boko Haram.