Google zai fara amfani da jirgi marar matuki

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jirgin dai ba shi da matuki

Kamfanin shafin intanet na matambayi ba ya bata wato Google ya sanar da kaddamar da jirgi marar matuki domin kai wa abokan huldatayya sakonni har gida.

Google dai ya fito da shi wannan sabon tsari mai taken 'Project Wing' ne dai da manufar daukar kaya ya kuma dangana su ga masu su har gidajensu ko kuma wuraren da suke son a kai musu.

A shekarar 2017 ne dai ake saran wannan jirgin zai fara aiki.

Sai dai kuma kawo yanzu ba bu wani karin bayani dangane da yadda sigar jirgin mara matuki za ta kasance.

Kamfanin na Google dai ya fito da wannan fasahar ne domin amfanin ma'aikatan kamfanin kuma an yi gwajin tashin jirgin, a kasar Australia.

Rahotannin farko farko dai sun ce za a iya amfani da jiragen da kamfanin ya yi wajen kai dauki kamar abinci ko magani ga mutane yayin afkuwar bala'o'i.

Shi dai jirgi mara matukin na Google zai iya tashi sama kuma ya yi shawagi har ma ya jejjefa kayayyaki zuwa kasa.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jirgin zai dinga kai wa mutane kayan da suka saya ne har gida.

Sauran kamfanoni da suka fice a harkar intanet kamar Amazon da Alibaba da dai sauransu su ma suna kokarin kirkiro irin wannan hanyar sada abokan huldatayya da kayan da suka siya.