NNPC ya tafka hasara

Hakkin mallakar hoto NNPC Website
Image caption Shugaban NNPC, Ibe Kachukwu

Kamfanin man fetur na Najeriya, NNPC, ya bada sanarwar faduwar fiye da naira biliyan biyar daga abubuwan da ya ke samarwa.

NNPC din na sarrafa man Diesel da kalanzir da kuma fetur.

Kamfanin ya ce ya yi cinikin fiye da naira biliyan 38 idan aka kwatanta da fiye da naira biliyan 44 da ya samu a watan Augustan wannan shekarar.

Daga watan Janairu zuwa watan Satumbar wannan shekarar, kamfanin na NNPC ya samu harajin naira 46 biliyan a kan man diesel da kalanzir da kuma man fetur.

Kamfanin NNPC tun bayan da aka nada Cif Emmanuel Kachukwu ya soma bayyana irin cinikin da yake yi a harkar man fetur na kasar a wani mataki na kawar da cin hanci da rashawa a kamfanin.

Tun bayan da ya soma mulki, shugaba Muhammadu Buhari ya yi alkawarin kawar da barna da dukiyar al'umma a kamfanin NNPC.